Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Mahalarta taron sun yi imanin cewa, saboda rashin adalci game da rarraba allurar rigakafi da wasu dalilai, ya zama wajibi a kara karfin samar da rigakafin a Afirka.
Manufar taron na kwanaki biyu, ita ce kara tattaunawa kan ci gaban samar da rigakafin.
Babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a taron cewa, sama da kashi 18 cikin 100 na sabbin alluran rigakafin COVID-19 suna zuwa kasashen mafiya karfin tattalin arziki na G20 ne, yayin da kasashe masu karamin karfi ke samun kashi 0.6 cikin 100 na allurar rigakafi a duniya.
Rashin adalci dangane da rabon alluran rigakafin na COVID-19, da bullar nau’in cutar na Omicron, ya nuna muhimmancin inganta karfin samar da allurar rigakafi a Afirka.
342/